Isa ga babban shafi
Tennis

Serena da Muguruza sun kai wasan karshe a Wimbledon

Serena Williams ta kai zagayen karshe a gasar Wimbledon bayan ta casa Maria sharapova a wasan dab da na karshe da suka fafata a jiya Alhamis. Yanzu Serena za ta hadu ne da Gerbine Muguruza da ta doke Agnieszka Radwanska a jiya Alhamis.

Serena Williams ta Amurka ta doke Maria Sharapova ta Rasha sau 17
Serena Williams ta Amurka ta doke Maria Sharapova ta Rasha sau 17 REUTERS/Toby Melville
Talla

Wannan ne karo na 17 da Serena ke lallasa Sharapova a haduwarsu a wasan Tennis.

Wannan ne kuma karo na 8 da Serena ke kai wa zagayen karshe a Wimbledon daya daga cikin gasa mafi girma da tsufa da stokar kudi a Tennis.

Sau 25 ke nan Serena na ka iwa zagayen karshe a manyan gasannin Tennis na Gram slams da suka kunshi Wimbledon da Australian Open da US Open da French Open.

Serena kuma na harin lashe kofunan manyan gasannin guda hudu a shekara guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.