Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA-Blazer ya tabbatar da karban cin hanci daga Afrika ta kudu

Tsohon babban jami’in hukumar kwallon kafa ta duniya, Chuck Blazer ya tabbar da karban cin hanci da suka yi n tare da wasu mambobin kwamitin zartarwa na FIFA dangane da bai wa Kasar Afrika ta kudu damar daukan bakwancin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010.

Tsohon babban Jami'in hukumar FIFA Chuck Blazer
Tsohon babban Jami'in hukumar FIFA Chuck Blazer AFP PHOTO / PETER KOHALMI
Talla

Blazer dan asalin kasar amurka ya kara da cewa shi ya yi hanyar karban cin hanci a gasar kofin duniya da aka gudanar a shekara ta 1998 kuma an bayyana ikirarin Blazer ne, wani sabon rahoto da Amurka ta fitar inda ya amince da tuhumar da ake masa na laifuka dabam dabam har goma.

Kasar Amurka ce ta bukaci gudanar da bincike dangane da badakakalar cin hanci da rashawa data dabaibaye hukumar kwalon kafa ta duniya, lamarin daya sa Sepp Blatter shugaban hukumar ya fuskaci matsalar da ta kai shi ga yin murabus daga mukaminsa.

A makon daya gabata ne dai masu shigar da kara na Amurka suka bukaci gurfanar da wasu manyan Jami’an FIFA 14 na da, da yanzu sakamkon zarginsu da hannu dumu dumu a karban cin hanci kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 150 cikin shekaru 24 yayin da tuni aka binciki mutane 4 daga cikinsu da shi kansa Chuck Blazer.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.