Isa ga babban shafi
FIFA

Blatter ya yi murabus a matsayin Shugaban FIFA

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, Sepp Blatter ya bayyana yin murabus a yau Talata daga mukaminsa sakamakon matsin lamba da ya ke fuskanta akan badakalar rashawa da ta dabaibaye hukumar. Blatter mai shekaru 79 na haihuwa ya shafe shekaru 17 yana jagorantar FIFA kuma a ranar Juma’a ne aka sake zabensa a wa’adi na biyar.

Shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter
Shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Blatter ya ce za a kira taron gaggawa domin zaben sabon shugaban FIFA.

Akwai manyan Jami’an FIFA 14 da Amurka ke tuhuma da karbar cin hanci wajen ba Qatar da Rasha damar karbar bakuncin gasar cin kofin Duniya a 2019 da 2022.

FIFA kuma ta amsa cewa Jami’inta Jack Warner ya karbi kudade dala Miliyan 10 daga hannun Afrika ta kudu domin ba kasar damar karbar bakuncin gasar cin kofin Duniya a 2010.

Amma hukumar ta wanke sakatarenta Jerome Valcke da hannu kan badakalar.

A cikin sanarwar da FIFA ta fitar a yau Talata, Hukumar tace babu hannun Sakatare Janar na hukumar amma ta tabbatar da cewa Afrika ta kudu ta aikawa Warner da kudaden wanda a lokacin shi ne shugaban kwallon kafa a yankin Amurka da Caribbean.

Warner dai na cikin mutane 14 da ake tuhuma da laifin karbar cin hanci da ya kai kudi dala miliyan 150.

FIFA kuma ta fitar da sanarwar ne bayan Jaridar New York Times ta kwarmato cewa na hannun damar Blatter ya karbi kudaden daga Afrika ta kudu.

Duk da FIFA ta karyata zargin amma kamfanin dillacin labaran Birtaniya ya ruwaito cewa Jarome Valcke yana da masaniya akan kudaden da Afrika ta kudu ta aika wa FIFA domin samun karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2010.

Masu ruwa da tsaki kan sha’anin Kwallon kafa a Turai na ganin duk da babu hujjoji da suka tabbatar da Blatter na hannu kan badakalar cin hancin, amma karkashin jagorancinsa aka bata sunan hukumar FIFA.

Shugaban Hukumar Kwallon kafa na Turai Michel Platini yana ganin ya dace Blatter ya yi murabus domin tsabtace hukumar FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.