Isa ga babban shafi
FIFA

Warner ya yi hasashen matsalar FIFA shekaru 4 da suka wuce

A shekara ta 2011 ne, tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Jack Warner ya gargadi cewa hukumar za ta fuskanci gagarumar matsala daya kwatan da ambaliyar tsunami

Jack Warne, tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya.
Jack Warne, tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya. REUTERS/Andrea De Silva
Talla

A lokacin da ya yi fama da zargin siyan kuri’u daga yankin Carribean a zaben FIFA shekaru 4 da suka wuce, warner ya bayyana cewa nanda wasu yan lokuta kalilan wata gagarumar matsala zata dabaibaye hukumar kwallon kafa ta duniya lamarin da zai girgirza hukumar, kuma jim kadan da fadin haka ne yayi murabus daga mukaminsa na mataimakin shugaban hukumar FIFA a watan yunin shekara ta 2011.

Warner dan asalin kasar Trinidad and Tobago na daya daga cikin manyan jami’an hukumar FIFA 14 na da da yanzu da hukumomin Kasar Amurka ke zargi da hannu a karban laifin cin da yawansa ya kai dalar Amuka miliyan 150, yayin da aka danganta shi a matsayin jigon da ya haifarwa hukumar matasalar da ta tsinci kanta a ciki, har ta kai ga murabus din da Sepp Blatter ya yi daga kujerarsa ta shugabacin FIFA.

A makon da ya gabata ne jami’an tsaro suka danke waner a Trinidad and Tobago duk da dai daga bisani an yi belinsa akan kudin amurka dala dubu 400 yayin da yake cigaba da kokarin wanke kansa da zargin na cin hanci da rashawa.

To sai dai kuma yanzu haka , Warner na cikin mutane shida da ‘yan sanda kasa da kasa wato Interpol ke nema ruwa a jallo domin fuskantar tuhuma.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.