Isa ga babban shafi
Spain

Rafael Benitez ne sabon kocin Real Madrid

Real Madrid ta sanar da kulla yarjejeniyar shekaru uku da Rafael Benitez a matsayin sabon kocinta a yau Laraba bayan ta sallami Carlo Ancelotti saboda ya gaza lashewa kungiyar kofi a bana. Real Madrid ta sanar a shafinta na Intanet cewa Benitez ne zai jagoranci kungiyar a kakar wasanni uku masu zuwa.

SAbon kocin Real Madrid Rafael Benitez
SAbon kocin Real Madrid Rafael Benitez Reuters
Talla

Benitez wanda ya bayyana yin bankawana da Kungiyar Napoli a bana yanzu zai dawo Spain inda ya lashe wa Valencia kofin La liga guda biyu a 2001 da 2004.

Tun barinsa daga Valencia zuwa Liverpool shekaru 11 da suka gabata, Benitez bai lashe kofin Lig ba. Ko da ya ke ya lashe wa Liverpool kofin gasar zakarun Turai da kofin FA da babban kofin Super na Turai a 2006.

Wasu na ganin Real Madrid ta yi saki-na dafe, bayan ta sallami Carlo Ancelotti wanda ya lashe ma ta kofin gasar zakarun Turai karo na 10.

Amma masu sharhi na ganin Benitez kwararre ne wanda ya jagoranci manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai da suka hada da Chelsea da Inter Milan da Napoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.