Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Xavi zai koma Qatar

Jagoran Barcelona Xavi Hernandez zai fice kungiyar da ya dade yana taka kwallo tun kuruciyarsa zuwa kasar Qatar idan an kammala kakar bana.Mahaifinsa ne Joaquin Hernandez ya kwarmata wa wata kafar rediyo a Spain akan dan wasan zai koma taka kwallo a kungiyar Al Sadd ta Qatar.

Dan wasan Barcelona Xavi Hernandez
Dan wasan Barcelona Xavi Hernandez REUTERS/Albert Gea
Talla

Xavi na cikin zaratan ‘Yan wasan Barcelona da tarihi ba zai taba mantawa da su ba, haka ma a Spain domin yana cikin wadanda suka lashe wa kasar Kofin Turai da kuma kofin duniya da aka gudanar a Afrika ta kudu a 2010.

Yanzu haka kuma ya taimakawa Barcelona lashe kofin La liga a bana, tare da taimakawa kungiyar zuwa zagayen karshe a Copa del Ray da gasar Zakarun Turai.

Mahaifinsa ya ce yarjejeniyar ta shafi ba Xavi damar taka kwallo a kungiyar tare da ba shi damar fara horo a matsayin mai horar da ‘yan wasa.

Jaridar wasanni ta El Mundo Deportivo ta ruwaito cewa a jibi Alhamis ne Xavi zai yi taron manema labarai inda zai bayyana matakinsa na yin bankwana da Barcelona.

Xavi dai ya nemi ficewa ne a bana duk da cewa sai karshen kakar badi ne yarjejeniyarsa za ta kawo karshe.

Xavi yana da shekaru 11 na haihuwa ya fara taka kwallo a Barcelona a shekarar 1991, kuma ya yi haskawa 760, wanda ya fi kowane dan wasa haskawa a tarihin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.