Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Bale na fuskantar suka a Madrid

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya soki wakilin dan wasansa Gareth Bale wanda ya yi zargin cewa rashin ba dan wasan kwallo a fili shi ne ya haifar masa da rashin nuna wata bajinta a bana.

Gareth Bale na Real Madrid
Gareth Bale na Real Madrid
Talla

A lokacin da ya ke mayar da martani Ancelotti yace Jonathan Barnett wakilin Bale ya cika surutu.

Bale dai shi ne tsadadden dan wasa a duniya wanda Real Madrid ta sayo daga Tottenham a 2013, amma dan wasan na fuskantar suka game da yadda kwallo ta ki aurensa a Madrid, musamman bayan Juventus ta doke su 2 da 1.

Amma Ancelotti ya kare dan wasansa inda yace Bale ya jefa kwallo a raga a wasan karshe da suka lashe kofin gasar zakarun Turai karo na 10 a kakar da ta gabata.

Rahotanni dai na cewa Bale wanda Baturen Birtaniya ne yana fuskantar wariya saboda bai iya harshen Sifaniyanci ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.