Isa ga babban shafi
Ingila

Arsenal ta lashe kofin FA

Kungiyar Arsenal ta lashe kofin FA na Ingila bayan ta doke Hull City ci 3 da 2 a fafatawar karshe da suka yi a filin wasa na Wembley. Aaron Ramsey ne ya zira wa Arsenal kwallo ta uku a ragar Hull wanda ya ba kungiyar nasarar lashe kofi a karon farko tsawon shekaru 9.

'Yan wasan Arsenal suna murnan lashe kofin FA a Ingila
'Yan wasan Arsenal suna murnan lashe kofin FA a Ingila Reuters
Talla

Arsene Wenger ya bukaci ‘Yan wasan shi na Arsenal su yi amfani da nasarar da suka samu a matsayin wani mataki na bude kofar samun wasu nasarori anan gaba.

A cewar Arsene Wenger lashe kofin na FA da suka yi a karshen mako wani tubali ne na gina sabuwar Arsenal a kaka mai kamawa.

Arsenal ta lashe kofin FA ne karo na 11 daidai da Manchester United kuma wannan shi ne kofin FA na biyar da Arsene Wenger ya lashe bayan kwashe shekaru 9 yana fuskantar barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.