Isa ga babban shafi
Ingila

Ashley Cole ya yi wa Ingila ritaya

Ashley Cole na Chelsea ya bayyana yin ritaya daga bugawa kasar shi Ingila wasa bayan Roy Hodgson da ke horar da ‘Yan wasan kasar ya ki gayyatarsa zuwa gasar cin kofin duniya a Brazil. Wannan kuma mataki ne da kocin na Ingila ya dauka na tafiya da matasan ‘Yan wasa.

Ashley Cole sanye da rigar Ingila
Ashley Cole sanye da rigar Ingila Reuters
Talla

Kuma a sakonsa bayan jin labarin ba za’a da shi ba, Ashley Cole ya yi wa Ingila fatan alheri.

Dan wasan dai ya fuskanci baraka ne tun a kungiyar shi ta Chelsea inda Mourinho ke ajiye shi a benci.

Cole ya kwashe shekaru sama da 10 yana takawa Ingila kwallo tun a 2001 da ya yi haskawar farko a karawa da tsakanin Ingila da Albania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.