Isa ga babban shafi
Premier League

Manchester City ta lashe Premier

A gida, Manchester City ta lashe kofin Premier bayan ta doke West Ham ci 2-0 a jiya lahadi. City ta lashe kofin ne karo na biyu a kaka uku, kuma ta lashe kofin ne da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool da ta doke Newcastle United ci 2-1.

'Yan wasan Manchester City suna murnar lashe kofin Premier a Ingila
'Yan wasan Manchester City suna murnar lashe kofin Premier a Ingila REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Tottenham ta samu shiga gasar Turai ta Europa League bayan ta doke Aston Villa, hakan kuma ke nuna za’a yi wasannin Turai a kaka mai kamawa ba tare da Manchester United ba a karon farko tun kakar ta 1989 -90.

Manchester City da Liverpool da Chelsea da Arsenal ne zasu wakilci Ingila a gasar Zakarun Turai.

Chelsea da ke matsayi na uku ta doke Cardiff ne ci 2-1, kuma tuni aka yi waje da Cardiff a gasar ta Premier da ita da Norwich City da ta sha kashi a hannun Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.