Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya zama gwarzon dan kwallon shekara ta 2013

A cikin daren jiya ne hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta fitar da sunayen wadanda suka fi taka rawa a fagen kwallon kafa a cikin shekarar da ta gabata wato 2013 a duniya. 

Ronaldo dauke da kwallon Ballon D'Or na 2013
Ronaldo dauke da kwallon Ballon D'Or na 2013 REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

An dai bayyana sunayen mutanen ne a wani gagarumin buki da aka gudanar a cibiyar wannan hukuma da ke birnin Zurich, inda Christiano Ronaldo dan kasar Portigal sannan kuma mai bugawa Club din Real Madrid ya zaman gwarzon dan wasa na duniya a bangaren maza.

Sai kuma Nadine Angerer ‘yar kasar Jamus wadda ta zama shahrarriyar ‘yar kwallon kafa ta duniya a bangaren mata, Hupp Heynckes na Bayern Munich da ke kasar Jamus, shi ne ya samu kyautar shahrarren koci ko kuma mai horas da ‘yan wasa na duniya a bangaren maza, yayin da Sylvia Neid ita ma ‘yar kasar Jamus ta samu wannan matsayi a bangaren mata.

An kuma bayar da wasu kyaututuka da dama a lokacin wannan biki na jiya, da suka hada da wanda ya fi zura kwallon da ta fi bai wa kowa sha’awa a cikin shekarar da ta gabata, tukuincin da aka bai wa Zlatan Ibrahimovic na kasar Sweden, sakamakon kwallon da ya jefa a ragar Ingila a lokacin da suke karawa a matsayin wasan sada zumunci.

 

Jacque Rogge dan kasar Belgium, wanda kuma shi ne tsohon shugaban Kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya ya samu kyautar gwarzon shugaba a harkar kwallon kafa, yayin da shahrarren dan kwallon duniyar nan wato Pele na kasar Brazil ya samu kyautar girmama daga hukumar ta FIFIA duk a cikin daren jiya.

Har ila yau an bayyana sunayen shahrarrun ‘yan wasa 11 daga sassa daban daban na duniya a matsayin ‘yan wasa na Tim Fifa, wadanda aka zaban kuwa su ne

Manuel Neuer (Bayern Munich)
Dani Alves (Barcelona)
Thiago Silva (PSG)
Sergio Ramos (Real Madrid)
Da kuma
Philipp Lahm (Bayern Munich)

Sauran kuwa su ne
Andres Iniesta (Barcelona)
Franck Ribery (Bayern Munich)
Xavi (Barcelona)
Cristiano Ronaldo (Real Madrid)
Da Zlatan Ibrahimovic (PSG) sai kuma
Lionel Messi na (Barcelona)

To wani abu a game da kyautar gwarzon shekara na kwallon kafar kuwa shi ne, Ronaldo ya samu wannan nasara ce da maki 1,365, wato a gaban Lionel Messi mai maki 1,205, sai Frank Ribery mai maki 1,127.

A cikin shekarar ta 2013 dai Ronaldo ya zura kwallaye 66 a raga a wasanni 56 da ya buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.