Isa ga babban shafi
FIFA

Ronaldo na iya sake zama Gwarzon duniya a bana

Cristiano Ronaldo wanda ya dade yana yi wa Messi Galadima, dan wasan yana iya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya da za’a bayyana a yau Litinin a birnin Zurich saboda yawan kwallayen da ya zirara a raga.

Cristiano Ronaldo yana murnar zira kwallon shi ta biyu a ragar Celta Vigo a La liga a Santiago Bernabeu
Cristiano Ronaldo yana murnar zira kwallon shi ta biyu a ragar Celta Vigo a La liga a Santiago Bernabeu REUTERS/Andrea Comas
Talla

Masu horar da ‘Yan wasa ne na kasashen duniya da jagororin kasashe da ‘Yan jarida ke jefa kuri’ar zaben Gwarzon Dan wasan Duniya na hukumar FIFA tsakanin ‘Yan wasa uku.

A bana Cristiano Ronaldo yana takarar gwarzon duniya ne tsakanin shi da Lionel Messi da Franck Ribery.

Karo hudu Lionel Messi na Argentina yana lashe kyautar amma a bana Cristiano ya fi shi kwarin gwaiwa duk da bai lashe kofi ba a 2013.

Cristiano wanda ya taba lashe kyautar a 2008 yanzu haka yana da jimillar kwallaye 66 a wasannin da ya buga wa Portugal da kungiyar shi Real Madrid.

Kodayake babu kofin da Ronaldo ya lashe a 2013 amma kafin karewar shekara, Ronaldo ya jefa kwallaye uku har sau biyar hadi da kwallayen da ya jefa a ragar Sweden a watan Nuwamba a wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya a Brazil.

Amma Ribery na iya haramtawa Ronaldo kyautar saboda yawan kofunan da dan wasan na Faransa ya lashe wa Bayern Munich guda biyar da suka hada da Kofin Bundesliga da kofin Jamus da kofin zakarun Turai da kofin Super na Turai da kuma kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa a Morocco.

Lionel Messi kuma yana iya dogaro da kofin La liga da ya lashe wa Barcleona a 2013 kuma shi ne ke da yawan kwallaye 46 a gasar.

Akwai kuma gwarzon mai horar da ‘yan wasa na duniya da za’a zaba tsakanin Sir Alex Ferguson tsohon kocin Manchester United da Jupp Heynckes tsohon mai horar da ‘Yan wasan Bayern Munich wanda ya lashe kofin zakarun Turai da kuma Klopp takwaransa na Borussia Dortmund.

Akwai jaruma da za’a zaba a bangaren mata tsakanin Nadine Angerer ta Jamus da Marta ta Brazil da kuma Abby Wambach ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.