Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Ronaldo na Brazil ya fi kaunar Messi fiye da Cristiano

Ronaldo na Brazil, yace a ra’ayin shi tsakanin Messi ko Ronaldo na Portugal ya kamata a zabi gwarzon duniya a bana wadanda yace ‘Yan wasan biyu sune gagara gasa ba tare da ya anbato sunan Franck Ribery ba wanda ake ganin zai iya lashe kyautar bayan ya doke Messi da Ronaldo a takarar gwarzon Turai.

Ronaldo Tsohon dan wasan Brazil
Ronaldo Tsohon dan wasan Brazil © RFI
Talla

A lokacin da ya ke zantawa da wata kafar Telebijin ta wasanni da ake kira “Fenomeno”, Tsohon dan wasan na Brazil yace ya fi ra’ayin Messi fiye da Ronaldo saboda wasu dalilai da ya yi la’akari da su.

Sai dai kuma Messi wanda ya kafa tarihin lashe kyautar gwarzon duniya sau hudu, a bana Ronaldo da Ribery sun fi shi kwarin gwiwar lashe kyautar musamman Ribery wanda ya lashe kofuna 5 a 2013.

A ranar 13 ga watan Janairu ne za’a bayyana sunan wanda ya lashe kyautar a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.