Isa ga babban shafi
FIFA

Messi da Ronaldo da Ribery ke takarar gwarzon duniya

Hukumar kwallon duniya FIFA ta tsame sunayen Lionel Messi da Franck Ribery da Cristiano Ronaldo a matsayin wadanda cikinsu za’a zabi gwarzon dan wasan duniya a bana. A ranar 13 ga watan Janairu ne za’a bayyana sunan dan wasan da ya lashe kyautar ta Ballon d'Or a birnin Zurich.

Lionel Messi da Frank Ribery da Cristiano Ronaldo wadanda za'a zabi gwarzon dan wasan duniya a tsakaninsu
Lionel Messi da Frank Ribery da Cristiano Ronaldo wadanda za'a zabi gwarzon dan wasan duniya a tsakaninsu www.uefa.org
Talla

Sau hudu ne Messi ke lashe kyautar gwarzon na duniya yayin da Ronaldo ya lashe kyautar sau daya.

Amma Franck Ribery na Faransa ana hasashen zai iya lashe kyautar a bana saboda tarin kofunan da ya lashe a kaka da ta gabata da suka hada da kofin zakarun Turai da kofin Jamus da kofin Bundesliga da kuma Super Kofi na Turai.

Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson yana cikin jerin masu horar da ‘yan wasa da za’a zabi gwarzo a bana.

Ferguson yana takara ne tsakanin shi da kocin Bayern Munich Jupp Heynckes da kuma kocin Borussia Dortmund Jurgen Klopp.

Tun bayan da Ferguson ya yi ritaya ya ke fuskantar suka musamman daga tsoffin ‘yan wasan shi da ya horar a Old Trafford.

A wata hira da za’a yada a gobe Talata tsohon Kaftin na Manchester Roy Keane yace ya fi jin dadin aiki tare da Tsohon kocin shi Brian Clough na Nottingham Forest, fiye da Ferguson saboda karfi da kaka-gida da Ferguson ke nunawa ga ‘yan wasa.

A dalilin Ferguson ne Roy Keane ya fice Manchester tun lokacin da suka fara samun sabani a 2005.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.