Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Manchester United za ta fuskanci kalubalen da ba ta taba fuskanta ba – Rio Ferdinand

Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand ya ce kungiyar za ta fuskanci kalubalen da ba ta taba fuskanta ba a tashin farko a Gasar Premier saboda wasannin guda biyar na farko da za su buga a sabuwar kakar wasa da za a shiga sun hada da karawa da kungiyoyin Chelsea, da Liverpool da kuma Manchester City.

Dan wasan Manchester United, Rio Ferdinand
Dan wasan Manchester United, Rio Ferdinand
Talla

Man U. za ta fara karawa ne da Swansea City a ranar 17 ga watan Agusta inda za ta kai mata ziyara, wanda kuma Ferdinand din ya ce jan aiki ne.

Kungiyar ta Manchester kamar yadda rahotanni ke nunawa ta bayyana cewa kungiyoyin Chelsea da Manchester City sun kasance kungiyoyin da za su iya kawo musu cikas wajen ci gaba da mallake kofin gasar ta Premier.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.