Isa ga babban shafi
Premier League

Rio Ferdinand ya yi ritaya daga buga wasan kasa da kasa

Dan wasan Manchester United da kasar Ingila, Rio Ferdinand ya ce lokacin ya yi da zai yi ritaya daga buga wasan kasa da kasa ga kasarsa ta Ingila. A cewar Ferdinand zai yi hakan ne domin ya mai da hankali ga bugawa kungiyarsa ta Manchester United.  

Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand
Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Dan shekaru 34, Ferdinand sau uku yana zuwa gasar Cin Kofin Duniya na World Cup, kuma kuma ya bugawa Ingila wasanni 81

Rabon da ya bugawa kungiyar ta Ingila kwallo tun a shekarar 2011 inda Ingila ta kara da Switzerland.

A yanzu haka Ferdinand ya na da burin ya sabunta kwatirakinsa da kungiyarsa ta Manchester United.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.