Isa ga babban shafi
Premier

Magoya bayan Arsenal sun bukaci Wenger yin cefanen ‘Yan wasa bayan samun riba

Kocin Arsenal zai fuskanci kalubalen bukatar sabbin zubin ‘Yan wasa bayan kungiyar ta bayar da sanarwar samun ribar kudi Fam Miliyan 17.8 a sakamakon jadawalin ribar kudin kungiyar da ake fitarwa a rabin shekara.

Arsène Wenger, Kocin kungiyar Arsenal
Arsène Wenger, Kocin kungiyar Arsenal REUTERS/Phil Noble
Talla

Wenger ya fuskanci suka saboda kin sayen ‘Yan wasa bayan kungiyar ta kwashe tsawon shekaru 8 tana Yunwar kofi wanda hakan ya sa ta yi hasarar zaratan ‘Yan wasanta irinsu Van Persie da Fabregas da Nasri.

A bara Arsenal ta samun ribar kudi Fam miliyan 24.5 sabanin bana inda kungiyar ta samu karin riba saboda cinikin Robin van Persie da kungiyar ta sayarwa Manchester United.

Kungiyar magoya bayan Arsenal tana ganin samun ribar wata dama ce a ware kudi domin cefanen ‘Yan wasa.

Sai dai yanzu haka Arsenal ta sabunta kwangilar ‘Yan wasanta Jack Wilshere da Theo Walcott da Kieran Gibbs da Aaron Ramsey da Alex Oxlade-Chamberlain da kuma Carl Jenkinson.

A bana kungiyar ta ware kudi Fam Miliyan 40.9 inda ta yo cefanen sabbin ‘Yan wasa da suka hada Lukas Podolski da Santi Cazorla da Olivier Giroud da kuma Nacho Monreal da aka sayo daga kungiyar Malaga.

Amma duk da haka a bana wata karamar kungiyar ce ta yi waje da Arsenal a gasar FA, kuma yanzu Arsenal ta sa kafa guda a waje a Gasar Zakarun Turai bayan ta sha kashi a filin wasa na Emirate hannun Bayern Munich.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.