Isa ga babban shafi
Champions League

Bayern Munich ta lallasa Arsenal, Barca za ta kai wa Milan ziyara

A filin wasa na Emirates kungiyar Bayern Munich ta bi Arsenal har ida ta lallasa ta ci 1-3 a gasar zakarun Turai. Hakan ke nuna Arsenal ta kama hanyar ficewa gasar bayan ta fice FA da Carling da kuma kalubalen da ke gaban Arsenal a teburin Premier.

Mai tsaron gidan Arsenal  Wojciech Szczesny ya zube kasa bayan zira kwallo a ragar shi a filin wasa na Emirates
Mai tsaron gidan Arsenal Wojciech Szczesny ya zube kasa bayan zira kwallo a ragar shi a filin wasa na Emirates REUTERS/Eddie Keogh
Talla

FC Porto kuma ta doke Malaga ci 1-0 wanda ya bata damar buga wasanni 20 ba tare da samun galabarta ba a dukkanin wasannin da ta ke buga a bana.

Tsawon shekaru 8 ke nan Arsenal na yunwar Kofi.

Toni Kroos and Thomas Mueller da Mario Mandzukic ne suka zirawa Bayern Munich kwallayeta a raga yayin da kuma Lukas Podolski ya samu damar zirawa Arsenal kwallo daya a ragar Bayern Munich.

Kwallayen da Bayern ta zira a gidan Arsenal kwallaye ne masu tsada domin duk kwallo daya yana zaman kamar biyu ne, amma Theo Walcott yace sai sun yi da gaske.
Walcot

“Ina ganin a Gasar Zakarun Turai komi na iya faruwa, idan mun zira kwallo a raga muna iya tsira” inji Walcott.

A yau Laraba ne Barcelona za ta kai wa AC Milan Ziyara a San Siro.
A bara Barcelona ce ta yi waje da AC Milan a zagayen Kwata Fainal da kuma haduwarsu a zagayen kusa da karshe a 2006.

Didier Drogba na Cote d’Ivoire zai fara haskawa a tawagar Galatasaray inda za su kece raini da Schalke 04.

A gobe ne kuma Chelsea da ta lashe kofin Zakarun Turai a bara zata kara da kungiyar Berth a gasar Europa League bayan ficewa gasar zakarun Turai tun a zagayen farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.