Isa ga babban shafi
Premier

Tottenham ta hauro matsayi na uku a Teburin Premier

Gareth Bale ya taimakwa Andre Villas-Boas tsallakawa zuwa matsayi na uku a Teburin Premier bayan zira kwallon karshe da ya ba kungiyar Tottenham nasarar lallasa West Ham ci 3-2 a filin wasa na Upton Park.

Kocin Tottenham Andre Villas-Boas  ya rungume Dan wasan shi Gareth Bale wanda ya taimakwa kungiyar tsallakwa zuwa matsayi na uku a Teburin Premier bayan doke West Ham ci 3-2
Kocin Tottenham Andre Villas-Boas ya rungume Dan wasan shi Gareth Bale wanda ya taimakwa kungiyar tsallakwa zuwa matsayi na uku a Teburin Premier bayan doke West Ham ci 3-2 REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Tun da farko ne Bale ne ya fara zira kwallo a raga daga bisani ne kuma Andy Caroll ya barke kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida a ragar tottenham.

Joe Cole ne ya zira wa West Ham kwallo ta biyu amma Sigurdsson ne ya barke kwallo kafin Bale ya zira kwallo ta Uku da ya ba Tottenham nasara.

Yanzu tazarar maki biyu ne Tottenham ta ba Chelsea da ke matsayi na hudu a teburin Premier, sannan Tottenham yanzu ta ba Arsenal tazarar maki 5 da ke a matsayi na Biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.