Isa ga babban shafi
La liga

Ronaldo ya yi wa Madrid alkawalin nasarori a 2013

Cristiano Ronaldo ya yi wa Real Madrid alkawalin samun nasarori a shekarar 2013, tare da bayyana cewa za su yi kokarin mayar da martani ga tazarar da ke tsakaninsu da Barcelona a Tebur. Wannan kuma na zuwa ne bayan jagoran kungiyar Iker Casillas ya nemi magoya bayan Real Madrid su kwantar da hankalinsu sakamakon tazarar maki 16 da ke tsakanins da Barcelona

Cristiano Ronaldo, Dan wasan Real Madrid
Cristiano Ronaldo, Dan wasan Real Madrid
Talla

Sai dai kuma a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai Ronaldo ya amsa cewa sun fuskanci matsaloli amma yace yana ganin abubuwa zasu sauya a 2013.

Ronaldo dai be ce uffan ba game da tsawaita kwangilar shi da Real Madrid.

A daya bangaren, kungiyar Real Madrid tace an yi wa Pepe tiyata a idon kafar shi ta dama ba tare da bayyana lokacin da ake sa ran dan wasan zai murmuje ba.

Kocin Barceolona kuma Tito Vilanova ya kai wa ‘Yan wasan shi Ziyara a filin da suke horo a jiya Laraba, bayan ya fara murmujewa daga tiyatar da aka yi masa kasa da makwanni biyu.

Hakan dai ke nuna kocin yana gab da dawowa ci gaba da aikin horar da ‘yan wasan Barcelona.

An fitar da Jerin sunayen yan kwallon da suka fi zura kwallaye a raga a gasar kwallon kafar Primiya Ligue ta kasar Ingla, tun da farko soma gasar ya zuwa rana ta 21.
 

van Persie (Manchester United) ya jefa kwallaye 16
 

Suárez (Liverpool) ya jefa kwallaye 15
 

Ba (Newcastle), Michu (Swansea City) sun jefa kwallaye 13
 

Defoe (Tottenham) ya jefa kwallaye 10
 

Bale (Tottenham), Dzeko (Manchester City) sun jefa kwallaye 9
 

Sai kuma, Agüero (Manchester City), Chicharito (Manchester United), Fellaini (Everton), S. Fletcher (Sunderland), Lambert (Southampton), Walcott (Arsenal) wadanda suka jajjefa kwallaye 8

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Andre Villas-Boas a yau alhamis ya bayyana cewa. Har yanzu dan wasan tsakkiyar fagen kungiyar dan kasar Togo Emmanuel Adebayor bai yanke shawara ko zai halarci gasar cin kofin nahiyar afrika na 2013 ko kuma a a, kamar yadda ya sanar zai yi a watan December da ya gabata.

Mai yiyiwa ne kasar Zimbabwe ta janye daga gasar fitar da gwani na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, da za a yi a kasar Brazil a -2014, sakamakon matsalar rashin kudin da take fuskanta da zai iya hanata jigilar yan kwallonta zuwa kasar Masar a watan Maris mai zuwa, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Zimbabwe (Zifa) ya sanar da AFP.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.