Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Kocin Super Falcons, Ikhana ya ajiye aikinsa

Mai horar da ‘Yan wasan club din mata na Super Falcons a Najeriya, Kadiri Ikhana ya ajiye aikinsa a matsayinsa na mai horar da ‘Yan wasan. Wannan ajiye aiki da Ikhana ya yi, ya zo ne bayan, ‘Yan wasan na Super Falcons sun sha kayi a hanun ‘Yan wasan kasar Kamaru inda suka lallasa su a gasar zakarun Nahiyar Afrika na mata da aka buga a kasar Equatorial Guinea a wasan da aka buga na neman matsayi na uku. 

Kadir Ikhana
Kadir Ikhana leadership.ng
Talla

A satin daya gabata ne Super Falcons har ila yau ta sha wani kayin a hanun ‘Yan wasan Bayana Bayana na kasar Afrika ta Kudu a wasan kusa da na karshe inda aka lallasa su da ci daya da nema.

A cewar Ikhana, ya ajiye aikin nasa ne domin burinsa bai cika ba, inda ya kara da cewa, burinsa shine yaga cewa sun lashe kofin gasar.

Ya kuma kara da bada hakuri ga daukacin ‘Yan Najeriya inda ya nemi a gafarce shi.

A dai watan Aprilun da ya gabata ne, Ikhana ya saka hanu a wani kwatiraki na shekaru hudu, a matsayinsa na mai horar da ‘Yan wasan na Super Falcons, bayan ba a sabunta kwantirakin tsohuwar mai horar da ‘Yan wasan na Najeriya ba, wato Eucharia Uche.

A dai ranar Lahadin da ta gabata ne, mai masaukin baki, Equatorial Guinea, ta lashe gasar bayan ta doke Afrika ta Kudu da ci 4-1.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.