Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Drogba ya kulla yarjejeniya da Shenhua a China

Dan kasar Cote D’Ivoire Didier Drogba yace ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da Rabi da kungiyar Shanghai Shenhua ta kasar China, inda zai ci gaba da wasa da Nicolas Anelka abokin wasan shi a Chelsea.

Dan kasar Cote d'Ivoire  Didier Drogba sanye da rigar tsohuwar kungiyar Shi ta Chelsea
Dan kasar Cote d'Ivoire Didier Drogba sanye da rigar tsohuwar kungiyar Shi ta Chelsea Reuters
Talla

Rahotanni sun ce Drogba shi ne dan wasan da yafi kowa tsada a China domin zai karbi kudi Fan dubu Dari Biyu a mako.

“ A yau (Laraba) zan shaida ma ku na kulla yarjejeniyar shekaru Biyu da Rabi da kungiyar Shanghai Shenhua FC ta kasar China har zuwa shekarar 2014” inji Drogba a sanarwar da ya bayar a shafin shi na Intanet.

Droba yace zai fara horo da tawagar Shanghai Shenhua FC a China a watan Yuli.

Yanzu haka a shafin kungiyar Shanghai Shenhua an nuna hoton Drogba sanye da rigar kungiyar, kodayake har yanzu shugabannin kungiyar ba su ce komi ba game da yarjejeniyar.

A karshen kakar wasan bana ne Drogba ya yi bankwana da Chelsea ta Ingila bayan taimakawa kugniyar lashe kofin gasar Zakarun Turai karo na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.