Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Chelsea ta kammala cinikin Eden Hazard daga Lille

Eden Hazard yace ya yanke hukuncin komawa Chelsea ne bayan kungiyar ta lashe gasar zakarun Turai. A jiya Litinin ne kungiyar Chelsea ta kulla yarjejejniya da dan wasan akan kudi Fam Miliyan 32 daga kungiyar Lille ta Faransa.

Eden Hazard dan kasar Belgium da Chelsea ta kammala cinikinsa daga kungiyar Lille ta Faransa
Eden Hazard dan kasar Belgium da Chelsea ta kammala cinikinsa daga kungiyar Lille ta Faransa
Talla

Eden Hazard shi ne dan wasa na Farko da Chelsea ta fara cefane a kasuwar ‘Yan wasa bayan lashe kofin gasar zakarun Turai.

Da Farko dai ana alakanta dan wasan ne da Manchester United da City.

A shafin intanet na Chelsea, kungiyar tace dan wasan zai fara horo cikin tawagar Chelsea a watan Yuni bayan kammala binciken lafiyar shi.

Rahotanni sun ce Chelsea zata biya dan wasan kudin albashi kimanin Fam 170,000 a sati.

Har yanzu dai Fernando Torres ne Chelsea ta saya da tsada daga Liverpool akan kudi Fam Miliyan 50.

Di Matteo zai yi amfani ne da Hazard da Marin da Juan Mata tare da Torres a matsayin ‘Yan wasan shi na gaba.

Hazard ya taimakawa kungiyar Lille lashe kofin French League a shekarar 2011, kuma shi ne aka zaba gwarzon dan wasan Faransa a bara bayan ya zira kwallaye 20 a raga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.