Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Drogba zai kulla yarjejeniya da Shanghai Shenhua

Dan wasan kasar Cote d’Ivoire Didier Drogba yana gab da kulla yarjejeniya da kungiyar Shanghai Shenhua, ta kasar China, domin bin sahun abokin wasan shi a Chelsea Nicolas Anelka.

Dan kasar Cote d'Ivoire  Didier Drogba.
Dan kasar Cote d'Ivoire Didier Drogba. Mark Kolbe/Getty Images
Talla

Wakilin kungiyar, Zhu Jun ya shaidawa kamfanin dillacin labaran China na Xinhua cewa nan da ‘yan kwanaki ne Drogba zai bada sanarwar yarjejeniyar shi da Shanghai Shenhua a shafin shi na Internet.

An bayyana Drogba zai karbi kudi Fan Dubu dari biyu a mako.

Tuni dai Anelka ya bayyana bukatar ganin Drogba tare da shi a China.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.