Isa ga babban shafi
Wasanni

Ajin matsayin Hukumar FIFA

Wallafawa ranar:

Shirin Duniyar Wasannin ya yi bayani game da ajin matsayin kasashe a fagen kwallon kafa, matsayin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke fitarwa a kowane wata.

Didier Drogba dan kasar Cote d'Ivoire
Didier Drogba dan kasar Cote d'Ivoire Reuters/Louafi Larbi
Talla

Ajin matsayi da hukumar FIFA ta fitar a watan Afrilu har yanzu kasar Spain ce a matsayi na daya a duniya, amma kasar Holland ta koma matsayi na hudu, domin yanzu Jamus ce a matsayi na biyu, Uruguay matsayi na uku.

Portugal da Brazil da Ingila sune a matsayi na biyar da na shida da na bakwai.

Najeriya idon Afrika sai ci gaba da fudawa take yi a fagen tamola, domin daga matsayi na 57 a watan jiya, yanzu Najeriya ta koma a mastayi na 60 a duniya kuma matsayi na Goma a Afrika.

Kasar Cote d’Ivoire ce a matsayi na daya a Afrika amma kasa ta 15 a duniya.

Kasar Ghana ce a matsayi na biyu, kuma kasashe irinsu Algeria da Mali da Libya dukkaninu sun sha gaban Najeriya.

Zaku ji tabakin wasu ‘yan Najeriyar game da sakamakon matsayin na hukumar FIFA tare jin bayanin shugaban hukumar Kwallon kafa Alh Aminu Maigari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.