Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Masar ta doke Najeriya a wasan sada Zumunci

A kasar Daular Larabawa ‘yan wasan kasar Masar sun doke ‘yan wasan Najeriya ci 3-2 a wasan sada zumunci da aka gudanar a jiya. Stephen Keshi ne dai ya jagoranci ‘Yan wasan Super Eagle wadanda yawancin ‘yan wasa ne masu taka kwallo a gida Najeriya.

Tawagar 'Yan wasan Super Eagle
Tawagar 'Yan wasan Super Eagle Reuters
Talla

‘Yan wasan Super Eagle Sunday Mba da Kalu Uche suka zirawa Najeriya kwallayenta a raga, ‘Yan wasan Masar kuma Ahmed Temsah da Muhammed Abouterika da Hassan Mekki ne suka zirawa Masar kwallayenta a ragar Najeriya.

Najeriya da Masar sun buga wannan wasan ne domin kimtsawa bayan kasa shiga gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a kasashen Gabon da Equatorial Guinea.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.