Libya da Mali sun sha gaban Najeriya da Masar a fagen tamola
A ajin matsayi a duniya da hukumar FIFA ta fitar, kasar Jamus ta karbe matsayi na biyu daga hannun Holland, amma kasar Spain ce har yanzu a matasayi na daya a duniya, kasar Hollad ta koma matsayi na hudu amma Uraguay ce a matsayi na uku.
Wallafawa ranar:
A Nahiyar Afrika, Kasar Cote d’IVoire ce ke jagorancin kasashen a matsayi na daya amma matsayi na 15 a duniya. Kasar Ghana ce a matsayi na biyu amma ta 22 a duniya.
Kasashe irinsu Libya da Algeria da Mali da Gabon dukkaninsu suna gaban Najeriya da Masar da Africa ta kudu.
Domin Algeria ce a matsayi na uku, Mali a matsayi na hudu Zambia a matsayi na biyar Gabon a matsayi na shida Libya a matsayi na Bakwai.
Kasar Masar ce a matsayi na Takwas amma ta 55 a duniya. Najeriya kuma a matsayi na 10 a Afrika amma ta 60 a duniya.
Jerin matsayi a Nahiyar Afrika da hukumar FIFA ta fitar a ranar 11 ga watan Afrilu.
15 1 Côte d’Ivoire
22 2 Ghana
38 3 Algeria
39 4 Mali
40 5 Zambia
42 6 Gabon
46 7 Libya
55 8 Masar
57 9 Tunisia
60 10 Najeriya
71 15 Afrika ta Kudu
102 23 Malawi
107 28 Botswana
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu