Isa ga babban shafi
Brazil

Shugaban kwallon kafar Brazil ya yi murabus

Shugaban kwallon kafar kasar Brazil Ricardo Teixeira ya yi murabus wanda shi ne shugaban kwamitin shirya gasar cin kofin duniya da za’a gudanar a kasar a shekarar 2014. Ricardo Teixeira ya kwashe tsawon shekaru 23 a matsayin shugaban kwallon kafa a Brazil.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Brazil, Ricardo Teixeira, yana gaisawa da ronaldo tsohon dan wasan Brazil a lokacin da zasu gudanar da wani taron kwamitin shirya gasar cin kofin Duniya da Brazil zata dauki nauyi a shekarar 2014.
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Brazil, Ricardo Teixeira, yana gaisawa da ronaldo tsohon dan wasan Brazil a lokacin da zasu gudanar da wani taron kwamitin shirya gasar cin kofin Duniya da Brazil zata dauki nauyi a shekarar 2014. REUTERS/Sergio Moraes
Talla

Ricardo Teixeira mai shekaru 64 na haihuwa yana cikin manyan mutane da ake girmamawa a Brazil, kuma a makon jiya ne ya dauki hutu domin diba lafiyar shi. Amma yanzu hukumar kwallon kafar Brazil tace ya yi murabus ne saboda kula da lafiyar shi.

A shekarar 2015 ne ya kamata wa’adin shugabancin Ricardo Teixeira ya kawo karshe.

Akwai dai cacar baki da ta hada Teixeira da tsohon dan wasan Brazil Romario.

Kuma jin kadan bayan sanar da Murabus din Teixeira, Romario ya aika da sako a shafin shi na Twitter da Facebook cewa yanzu kwallon kafa a Brazil ta warke daga cutar Cancer da ta kama ta domin Ricardo Teixeira ya yi murabus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.