Kasashen yankin Caribbean sun kira taron gaggawa kan rikicin Haiti
Shugabannin kasashen yankin Caribbean sun yi kira da a gudanar da wani taron gaggawa a Jamaica tare da kasashen Amurka, Kanada da Faransa a gobe Litinin don neman hanyar fita daga tarzomar 'yan tawayen Haiti.
Wallafawa ranar:
Mambobin kungiyar sun kwashe watanni suna kokarin ganin 'yan siyasa a Haiti sun amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa ta rikon kwarya.
Duk da cewa kungiyar ta kasashe 15 ba ta yi nasara ba izuwa yanzu, cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Juma'a da ta gabata, ta ce har yanzu ta na kan bakanta na neman cimma wannan manufa.
Ko a ranar Jumma'a da ta gabata sai da gungun tsagerun 'yan Haiti masu adawa da gwamnati suka yi fito-na-fito da 'yan sandan kasar, rikicin da ya tilasta kungiyar kasashen na Caribbean kiran taron gaggawa domin kawo karshen wannan fita da ke neman daidaita kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu