Isa ga babban shafi

Adadin masu kwanan titi saboda rashin muhalli ya kai kololuwa a Birtaniya

Alkaluman mutane marasa muhalli da ke rayuwa a tituna ya karu a sassan Birtaniya, adadin da ofishin kididdiga ke cewa shi ne karon farko da ake ganin hauhawarsa sakamakon matsi da tsadar rayuwa a sassan kasar.

Yanayin tsadar rayuwa ya kai kololuwar da Birtaniya bata taba gani ba a tarihi cikin shekarun baya-bayan nan.
Yanayin tsadar rayuwa ya kai kololuwar da Birtaniya bata taba gani ba a tarihi cikin shekarun baya-bayan nan. AFP - VINCENZO PINTO
Talla

Alkaluman sun nuna cewa daga watanni ukun karshen 2023 zuwa yanzu adadin yawan mutanen da ke kwana a titunan Birtaniya ya karu daga dubu 3 da 570 zuwa 4 da 389.

A cewar hukumar kididdigar ya karu ne da kashi 23 yanayin da kasar ba ta taba ganin karuwarsa cikin gaggawa ba.

Wata kididdiga ta daban tan una yadda fiye da mutum dubu 1 da 200 suka nemi matsugunan wucin gadi mallakin gwamnati a sassan Birtaniyar cikin makwanni biyu kadai na watan Janairu.

Masana na alakanta karuwar masu kwanan titin a Birtaniya da yanayin tabarbarewar tattalin arzikin kasar wanda ya haddasa matsananciyar tsadar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.