Isa ga babban shafi

'Yan Afrika ta Kudu na zanga-zangar tsadar rayuwa

Dubban al’ummar Afrika ta kudu na gudanar da yajin aikin gama-gari a wani mataki na nuna adawa da yanayin tsadar rayuwa.

'Yan Afrika ta Kudu sun ce, ba za su iya jurewa tsadar rayuwa ba a kasar.
'Yan Afrika ta Kudu sun ce, ba za su iya jurewa tsadar rayuwa ba a kasar. © AP Photo/Odelyn Joseph
Talla

Manyan kungiyoyin kwadago na kasar 2 ne ke jagorantar  yajin aikin, inda suka bukaci kowanne bangare na kasar da ya shiga zanga-zangar domin nuna bacin rai kan matsalar rashin aikin yi, tsadar man fetur da wutar lantarki.

Kungiyoyin sun bukaci gwamnatin kasar ta rage farashin man fetur da kudin ruwa, sannan ta rika bada kudaden alawus-alawus.

Akalla kashi 3 cikin 4 na alummar Afrika ta kudu na fama da rashin aikin yi, kasar da a halin yanzu  ke fuskantar tabarbarewar tattalin arziki biyo bayan barkewar cutar Korona da kuma yakin Ukraine da ya barke sakamakon mamayar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.