Isa ga babban shafi

Macron ya sha alwashin sake karfafa Faransa daga koma bayan da ta fuskanta

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sha alwashin samar da sabuwar rayuwa ga kasar ta hanyar karfafata da nufin kawar da kalubalen da suka dabaibayeta, dai dai lokacin da ya ke da sauran fin shekaru 3 a wa’adinsa na karshe a mulkin kasar.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa yayin jawabinsa gaban taron manema labarai.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa yayin jawabinsa gaban taron manema labarai. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

A wani taron manema labarai da ba safai shugaban na Faransa ya saba gudanarwa ba, Macron ya ce zai tabbatar da sake inganta Faransa a dukkan matakai, yana mai alkawarta tabbatar da adalci ga kowanne bangare na al’ummar kasar ta hanyar sauke nauyin da ke kansa.

Shugaba Macron na fuskantar manyan kalubale a mulkinsa baya ga jerin tarnaki daga babbar jam’iyyar adawa ta masu tsattsauran ra’ayi dai dai lokacin da ya ke da fin shekaru 3 a kujerar mulkin kasar ta Turai.

A makon jiya, Macron ya sanar da sabuwar majalisa tare da nada Gabriel Attal mai shekaru 34 a matsayin Firaminista wanda ya mayar da shi Firaminista mafi karanci shekaru a Faransar.

Karkashin sabbin dokokin da Macron ya gabatar daga yanzu Faransar za ta fara tilastawa dalibai sanya kayan makaranta baya ga wajabta koyon taken kasar ga dukkan dalibai sai kuma mayar da darasin drama a matsayin na dole a dukkan makarantu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.