Isa ga babban shafi

Tesla ya janye motocinsa sama da miliyan guda da rabi saboda matsala

Kamfanin Tesla ya sanar da janye motocinsa masu amfani da wutan lantarki da ke neman gyara miliyan 1 da dubu 600, daga kasuwar China. 

Motocin Tesla
Motocin Tesla AP - Noah Berger
Talla

Hukumar dake kula da ingancin kayayakin kasuwar China da ta fitar da sanarwar a ranar juma'a, ta ce yanzu haka motocin Tesla masu lamba S, da X da 3 da kuma Y na a biranen Beijing da Shanghai, inda za a gyara su. 

Daga cikin motocin da su ka samu matsala, akwai dubu 7,538 da ke da matsalar da ta shafi na’urar bude kofa, wadanda aka kera su tsakanin ranar 26 ga watan Oktoban shekarar 2022 zuwa ranar 16 ga watan Nuwamban shekarar 2023 da ta shude. 

Hukumar ta kuma ce a cikin shekarar 2022 kusan motocin Tesla dubu 128 dake china ke bukatar gyara. 

Shugaban kamfanin na Tesla, Elon Musk ya kulla alaka ta kut da kut da hukumomin China, duk kuwa da tsamin dangantakar dake tsakaninta da Amurka. Kasancewar China ce cibiyar da ake kera motocin na Tesla. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.