Faransa ta cafke wasu mutane 5 da take zargi da kitsa ta'addanci a kasar.
Mutane 5 ne aka kama a ranar juma’ar da ta gabata a yankin gabashin kasar Faransa, inda ake ci gaba da tsaresu a karkashin rundunar ma’aikatar leken asiri, a wani binciken ayukan ta’addanci da ta ke tuhumarsu da aikatawa, kamar yadda mai shigar da karar ayukan ta’addanci ya sanar.
Wallafawa ranar:
Wata majiyar ta kusa da kundin, ta sanar da AFP cewa, an kanga wa mutanen 5 kyaure ne, ba tare da yin wani karin haske kan irin zargin da ake yi masu ba.
A cewar majiyar, an yi kamun ne a safiyar ranar juma’ar da ta gabata a cikin gundumomin Meurthe-da-Moselle, dake cikin jihar Nancy, da kuma garuruwan dake kusa da juna, Vandœuvre-lès-Nancy da Toul.
Shi dai wannan samame ya zo ne a dai dai lokacin da ministan cikin gida Gérald Darmanin, a ranar juma’a ya yi kiran kantomomi, da su maida hankali sosai kan lamarin tsaro, albarkacin shagulgulan Christmas da sauran shagulgulan addinin da ake gudanarwa, sakamakon karuwar barazanar ayukan ta’addanci da ake ci gaba da fuskanta a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu