Isa ga babban shafi

Faransa ta rufe ofishin jakadancinta da ke Nijar

Faransa na shirin rufe ofishin jakadancinta da ke Jamhuriyar Nijar, inda ake ci gaba da nuna mata tsangwama tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin da ya gabata.

Jami'an tsaron Nijar na kewayawa a kusa da ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Yamai.
Jami'an tsaron Nijar na kewayawa a kusa da ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Yamai. AFP - -
Talla

Matakin rufe ofishin jakadancin na zuwa ne bayan dimbin ma'aikatan diflomasiyar Faransa sun fice daga kasar sakamakon hare-hare, abin da ya sa ofishin ya dakatar da aikace-aikacensa kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka bayyana.

Majiyoyin sun ce, bayan wani hari da aka kaddamar kan ofishin jakadancin a ranar 30 ga watan Yuli da kuma yadda sojojin kasar suka  toshe hanyoyin da ke kewayen harabar ginin ofishin, akasarin ma'aikatan diflomasiyyar sun fice daga kasar a karshen watan Satumba.

Wannan al'amari ne ya hana ofishin jakadancin ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda ya saba, abin da ya sa gwamnatin Faransa ta yanke shawarar rufe ofishin jakadancin.

Tuni aka sallami ma'aikata 'yan asalin Nijar da ke aiki a ofishin jakadancin bayan an yi musu ihsani kamar yadda majiyoyin na diflomasiyya suka tabbatar.

Danganta tsakanin Nijar da Faransa ta yi tsamin bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli, inda suka kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum.

Sojojin da suka kwace mulkin sun soke yarjeniyoyin tsaro da Faransa, yayin da suka kori jakadan kasar, inda kuma suka kulla alakar kut da kut da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.