Isa ga babban shafi
KWALON KAFA

Labarin wasanni: kocin Man City, ya bayyana tabbacin sake lashe kofin gasar premier League

Mai horar da kungiyar da kmwallon kafa ta Manchester City  Pep Guardiola yace yana da kwarin gwiwa zai lashe gasar firimiyar Ingila karo na 4 a jere a tarihin gasar.

Kocin Man City Pep Guardiola 2022
Kocin Man City Pep Guardiola 2022 AP - Dave Thompson
Talla

Manchester City sune ke rike da kambu na shekarar da ta gabata wanda shi ne kofin su na uku da suka dauyka a kakar wasannin na shekarar da ta gabata, amma sai dai wasu zaratán ‘yan wasan kungiyar na fama da rauni Wanda ake ganin shi ne zai zama babban kalubalen da zai kawo wa kungiuyar cikas a burin tan a kara  lashe wannan Kofi a kakar wasannin shekara ta 2023 da kuma 2024.

A baya-bayan nan kungiyar ta buga wasanni uku Wanda ta yi canjaras duk da wannan sakamakon Guardiola na da kwarin gwiwa lashe gasar inda yake aikewa abokan hamayyar sa cewa ba bu wata damuwa a tawagar sa.

Sai kuma labarin dake cewa, tsohon dan wasan Brazil da Barcelona Dani Alves zai fuskanci hukunci shekaru 12 a gidan yari bisa zargin fyade.

Dani Alves a na tsare da shi ne a gidan yari a Barcelona, tun watan Janairu bayan kama shi da kuma tuhumarsa da ake yi da laifin fyade, na hana tsohon dan wasan ayan na Barcelona da Juventus da ya nema beli har sau uku , kuma ana sa ran zai fuskanci shari’a a watan Fabarairu farkon shekara mai zuwa .

A cikin ‘yan makonin nan, mai gabatar da kara wadanda ke jagoranta shari’ar da ake yi wa Alves sun nemi a yanke wa dan wasan na Brazil hukuncin zaman gidan yari na shekaru 9, sai dai kuma wannan sai dai masu shigar da karar ba su gamsu da wannan bukatar ba domin sunce sheakeru 12 ya dace.

Shekaru 12 su ne hukunci wanda ya aikata fyade kamar yadda doka ta tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.