Isa ga babban shafi

Arda Turan ya fada komar 'yan damfara a Turkiya

Tsohon dan kwallon kafar nan Arda Turan ya fada komar ‘yan damfara a kasar Turkiya inda ya tabka asarar miliyoyin daloli.Turan ya ce an damfare sa kudade da yawan su yakai dalar Amurka miliyan goma sha uku 13m a kasar sa.Ya siga jerin  ‘yan kwallon kafa 18 da wani dan damfara ya samu nasara a kan su a kasar Turkiya.

tsohon dan wasan kungiyar Atleticio Madrid da Galatasaray
tsohon dan wasan kungiyar Atleticio Madrid da Galatasaray AFP/Archives
Talla

A wani mataki na kotu mai lamba 14 mai hukunta masu aiakata manyan laifuka a birnin Santambul ta fara bincike akai domin gano yadda wannan matsalar ta faru.

A na zargin wani darakatan bankin Denizbank Levent Secil Ezran da aikata wannan ta'asa, jami;in banin da ke da mukamin darakatan a na zargin sa da kwashe kudin da ya kai dala miliyan 44 na 'yan wasa a kalla su goma sha takwas 'yan asalin kasar Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.