Isa ga babban shafi

Ma'aikatan kamfanoni sama da 30 marasa takardun izini na yajin aiki a Faransa

A Faransa,daruruwan ma’aikatan da ba su da takardun aiki sun fara yajin aiki na bai daya a kamfanoni sama da 30 a wasu yankunan  Ile-de-France a safiyar yau Talata domin yin tir da wasu matakai ko tsare-tsare da nufin samu inci da neman  daidaito.

Wasu daga cikin  ma'aikata karkashin kungiyar CGT ta kasar Faransa
Wasu daga cikin ma'aikata karkashin kungiyar CGT ta kasar Faransa © AP/Thibault Camus
Talla

Akala mutane 500, galibi daga Afirka, sun mamaye kusan kamfanoni 33 da ke wadanan yankunan, galibi a cikin Paris da Seine-Saint-Denis.

 Wasu ma’aikatan 34 daga cikinsu sun shiga hedkwatar wani kamfanin samar da aikin yi na wucin gadi a Saint-Denis, wanda ake daukarsu aikin a matsayin masu tattara shara ko ma'aikatan gine-gine.

Masu boren tare da rakiyar masu fafutuka na ƙungiyoyin kwadago, sun nuna tutar CGT kuma sun yi alƙawarin mamaye wuraren har sai sun samu biyan bukata.

Wasu daga cikin bakin haure
Wasu daga cikin bakin haure AFP/Geoffroy Van der Hasselt

Yawancin masu yajin aiki na matsayin ma'aikata na wucin gadi ga 'yan kwangila, suna aiki da irin Kamfanon da suka hada da  Véolia, Chronopost da Carrefour.

Mamadou Kebé daya daga cikin masu magana da sunan masu bore ya ce, "muna so mu sa abubuwa su faru,"wanda ya samu sabani bayan yajin aikin shekara daya tsakanin Oktoba 2008 da 2009. "Waɗannan ma'aikata dole ne su sami damar jin daɗin haƙƙin kai da suke ba da gudummawarsu a bangaren da ya shafi biyan haraji," in ji Mamadou Kebé  wanda  yanzu ke jagorantar ƙungiyar shige da fice ta CGT 93.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga na kungiyar CGT a Faransa
Wasu daga cikin masu zanga-zanga na kungiyar CGT a Faransa AFP - SEBASTIEN SALOM-GOMIS

Wasu alkaluma da ake da su na nuni cewa tsakanin ma'aikata 7,000 zuwa 10,000 ake da su a wannan sashe na marar sa takardun aiki a kasar ta Faransa.

A Ile-de-Faransa, baƙi suna wakiltar kashi "40 zuwa 62% na ma'aikata ta bangaren ayukan gida, gine-gine, otal da abinci, tsaftacewa, tsaro da sassan abinci" , in ji ƙungiyar a cikin sanarwar da ta fitar a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.