Isa ga babban shafi

An gano bakin haure sama da 700 a gabar tekun Ingila

An gano bakin haure 755 a cikin kananan jiragen ruwa 14 da suka nufi gabar tekun kudancin Ingila, kamar yadda kididdigar ma'aikatar harkokin cikin gida ta Burtaniya ta nuna, mafi yawa da aka taba samu a rana guda kenan a bana.

Mutane yayin zanga-zanga a birnin Madrid kan mutuwar bakin-haure akalla 23 a ranar Juma'a yayin yunkurin na isa yankin Melilla na kasar Spain a ranar 26 ga Yuni, 2022.
Mutane yayin zanga-zanga a birnin Madrid kan mutuwar bakin-haure akalla 23 a ranar Juma'a yayin yunkurin na isa yankin Melilla na kasar Spain a ranar 26 ga Yuni, 2022. © REUTERS/Nacho Doce
Talla

Wadannan kwale-kwalen sun kawo adadin bakin haure a bana zuwa kusan 16,000, kuma ana samun karuwar adadin ne tun lokacin da aka kirga tafiye-tafiyen su a shekarar 2018 kawo yanzu zuwa 100,715.

Kididdiga ta karshe a 2023 ta bayyana cewa an samu kasa da kason da aka samua  shekarar bara, karon farko tun lokacin da matsalar ta fara girma shekaru goma da suka gabata.

Baki 299 ne kawai suka yi balaguro a cikin shekarar 2018, amma a cikin 2020 sun haura zuwa 8,466 yayin da a bara aka sami adadin masu shiga Turai zuwa 45,755.

Mafi karancin kididdiga a 2023 na iya kasancewa saboda watanni na musamman da aka samu na rashin kyawun yanayi, wanda ke hana tafiye-tafiye a cikin ruwa.

Hukumomin Faransa sun ce sun kara kaimi wajen aikin sintiri da sauran matakan dakile zirga-zirgar su, bayan Birtaniya ta amince a watan Maris na aika wa Faransar daruruwan miliyoyin Yuro a duk shekara don kawo karshen matsalar.

Hanyar da ta kasance daya daga cikin manyan hanyoyin jigilar kaya a duniya, ta kasance mai hatsari a lokuta da dama, inda da yawan bakin haure sukan nutse ne a cikin ruwa, tun daga shekaru goma da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.