Isa ga babban shafi

Zaben Slovakia na barazana ga hadin kan EU wajen bai wa Ukraine makamai

Al’ummar Slovakia na kada kuri’a a zaben ‘yan Majalisu yau Asabar, zaben da zai iya zama barazana ga dunkulewar kasashen Turai wajen tunkarar rikicin Ukraine, lura da yadda ake fafatawa tsakanin jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi da ke adawa da ci gaba da bai wa Ukraine makamai sai kuma jam’iyya mai goyon bayan kudirin kasashen yammaci.

Masu kada kuri'a a zaben Slovakia.
Masu kada kuri'a a zaben Slovakia. AP - Darko Bandic
Talla

Firaminista Robert Fico mai tsattsauran ra’ayi kai tsaye ya sha alwashin kawo karshen kudin da ya ce kasar na kashewa wajen bai wa Ukraine makamai.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a dai ta nuna yadda ake matsayin kan-kan-kan tsakanin bangarorin biyu, kuma wanda ya yi nasara kai tsaye zai samu damar kafa gwamnatin da za ta maye gurbin shugabancin rikon kwaryar da ke jagorantar kasar mai yawan jama’a miliyan 5 da rabi tun watan Mayun da ya gabata.

Guda cikin 'yan takarar zaben Slovakia  Robert Fico.
Guda cikin 'yan takarar zaben Slovakia Robert Fico. REUTERS - RADOVAN STOKLASA

Idan har Fico ya yi nasarar karbar ragamar kasar, kai tsaye Slovakia z ata bi sahun kasashen EU irinsu Hungary da ke kalubalantar ci gaba da bai wa Ukraine tallafi, dai dai lokacin da kungiyar ke fafutukar ganin ta samu cikakken hadin kai wajen kalubalantar Rasha.

Alkaluma dai na nuna cewa abu ne mai wuya ilahirin bangarorin biyu su iya samun rinjaye a zaben na yau, wanda ke nuna yiwuwar kafa gwamnatin hadaka tsakaninsu da kananun jam’iyyun da suka kunshi masu tsaka-tsakan ra’ayi.

Fico dai ya sha alwashin kawo karshen bai wa Ukraine makamai tare da zabar tsarin tattaunawa tsakanin shugabancin kungiyar da Rasha da nufin kawo karshen rikicin, tunanin da ya yi dai dai da kudirin Viktor Orban na Hungary wanda ya nemi shiga tattaunawa da Moscow amma EU ta yi watsi da kudirin.

Da misalin karfe 10 na daren yau ne dai za a kulle rumfuna kada kuri’ar kuma akwai fatan sanar da sakamako sa’o’I kalilan bayan kammala zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.