Isa ga babban shafi
Euro 2016

Wales ta doke Rasha, Slovakia ta rike Ingila

Wales da Ingila sun tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin Turai da ake gudanarwa a Faransa. Amma Wales ce ta jagoranci rukuninsu na B bayan ta doke Rasha ci 3 da 0.

Dan kasar Wales Gareth Bale na Real Madrid
Dan kasar Wales Gareth Bale na Real Madrid REUTERS/Regis Duvignau Livepic
Talla

Ingila kuma ta kasance matsayi na biyu bayan ta tashi wasa babu ci tsakaninta da Slovakia.

Gareth Bale da Aaron Ramsey da Neil Taylor ne suka jefa wa Wales kwallayenta a ragar Rasha.

Jagorantar rukunin dai ya taimakawa Wales kaucewa haduwa da wata babbar kasa, yayin da Ingila zata iya haduwa da kasar da ta jagoranci rukunin F, inda za ta iya haduwa da Portugal.

Bayan fitar da Rasha, Kocin kasar Leonid Slutsky ya ce zai yi murabus bayan rashin tabuka wani abin azo a gani a gasar cin kofin Turai.

Rasha ce dai ta karshe a rukunin B da maki guda.

Wasannin Euro 2016

A yau Talata Jamus da Ireland zasu fafata a birnin Paris, haka ma lokaci guda ne Poland zata kara da Ukraine a rukuninsu na C.

Daga bisani ne Spain za ta fafata da Croatia a Bordeaux, lokaci guda da Turkiya da Jamhuriyyar Czech za su fafata.

Jamus dai na neman maki guda ne domin samun wuri a zagaye na gaba.

Spain kuma sai ta yi kokarin doke Croatia domin jagorantar rukuninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.