Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta mayar da jagoran magoya bayan Rasha gida

Faransa ta mayar da jagoran magoya bayan Rasha gida saboda rikicin da ya barke tsakanin Rashawa da magoya bayan Ingila a gasar cin kofin kasashen Turai.

Wani dag cikin magoya bayan Rasha da ya shiga hannun jami'an tsaron Faransa
Wani dag cikin magoya bayan Rasha da ya shiga hannun jami'an tsaron Faransa
Talla

Alexander Shyprygin na cikin Rashawa 20 da hukumomin Faransa suka tirsasa mu su komawa kasarsu ta asali, a wani mataki na magance tashe-tashen hankulan da ake samu a dai dai lokacin da ake gudanar da wannan gasa ta Euro 2016 a Faransa.

An dai tsare mutanen ne a lokacin da suke kokarin zuwa birnin Lille daga Marseille domin kallon wasan da Rasha ta yi da Slovakia.

Sannan kuma akwai Rashawa guda uku da aka kulle a gidan yari har na tsawon shekaru biyu saboda samun su da laifin tayar da rikici a birnin Marseille.

Har ila yau an haramta wa mutanen shiga Faransa har na tsawon shekaru biyu yayin da gwamnatin Rasha ta nuna bacin ranta kan wannan matakin da aka dauka akan ‘yan kasarta kuma tuni ta kira jakadan Faransa a Rasha domin nuna fushinta.

Akwai yiwuwar za a dakatar da Rasha daga buga gasar ta Euro 2016 da zaran magoya bayanta sun sake haifar da tarzoma a filayen wasanni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.