Isa ga babban shafi
Euro 2016

Faransa ta doke Albania 2 da 0

Faransa ta samu tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin Turai da ake gudanarwa a kasar bayan ta doke Albania ci 2 da 0 a daren jiya Laraba.

Faransa ta tsallake zagaye na biyu a gasar cin kofin Turai
Faransa ta tsallake zagaye na biyu a gasar cin kofin Turai Reuters
Talla

Ana dab da kammala wasan ne Antoine Griezmann da Dimitri Payet suka kwaci Faransa a hannun Albania.

Wasannin Euro 2016

Yanzu Faransa ce saman teburin rukuninsu na A da maki shida Switzerland kuma da za ta hadu da Faransa a wasan rukuninsu na karshe ita ce ke matsayi na biyu da maki 4 bayan ta yi kunnen doki ci 1 da 1 da Romania.

Romania na iya sha idan har ta ci Albania kwallaye da yawa amma sai Faransa ta doke Switzerland.

A rukunin B kuma a yau Wales za ta kara da Ingila wasan da zai ja hankali a yau tsakanin kasashen biyu na Birttaniya.

Ingila dai za ta nemi doke Wales domin tsira a gasar bayan ta yi kunnen doki da Rasha a karawar farko.

Wales ce saman teburin rukuninsu na B kuma nasara akan Ingila zai tabbatar wa kasar nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Jamus za ta kara da Tsohuwar abokiyar gabarta Poland a yau Alhamis inda Robert Lewandowski zai hadu da abokan wasan shi na Bayern Munich

Ukraine kuma za ta fafata ne da Nothern Ireland.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.