Faransa ta umurci wasu cibiyoyi su kasance cikin shirin ko-ta-kwana saboda zafi
Faransa za ta sake fuskantar wani yanayi na tsananin zafi a cikin ‘yan kwanakin nan, inda aka yi hasashen cewar tsananin zafin zai zama mafi muni da aka samu a bazarar bana, lamarin da ya sa Hukumar Kula da Yanayi ta Kasar ta bukaci wasu hukumomi 19 su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
Wallafawa ranar:
A cewar hukumar, a karshen wannan makon ne za a samu tsanantar yanayin zafi, musamman a yankin kudancin tsakiyar kasar, inda ake sa ran daga ranar Lahadi, yanayin zafin a wasu lokuta zai rinka zarce maki 40 a ma’aunin yanayi a Kudu Maso Gabas, inda kuma za a ci gaba da samun haka har zuwa akalla tsakiyar mako mai zuwa.
Masu hasashen yanayin sun kuma ce, wannan ne zai zama yanayi na tsananin zafi a lokacin bazara da aka taba samu.
Wannan ne ya sa a Juma'ar nan, hukumar ta bukaci wasu cibiyoyin 19 su kasance cikin Shirin kota kwana, sabida tsananin zafin.
Ko a Alhamis din nan, sai da firaministar Faransa Elisabeth Borne ta kira wani kwarya-kwaryar taro, wanda a karshensa, gwamnati ta yanke shawarar samar da wata farfajiyar da za ta rinka bada bayanai, sannan a rika yada matakan kariyar da ya kamata al'umma su dauka a kafofin rediyo da kuma na talabijin din kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu