Isa ga babban shafi

MDD ta yi gargadin yiwuwar 2023 ta zama shekara mafi tsananin zafi a tarihi

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kasashen yankin arewacin duniya za su ci gaba da ganin tsananin zafi sakamakon dumamar yanayi da ke ci gaba da ta’azzara, gargadin da ke zuwa a dai dai lokacin da tuni nahiyar Turai da arewacin Amurka da kuma wasu sassa a Asiya suka fara ji a jikinsu.

Tsanani na ci gaba da kai wa kololuwa a shekarar da muke ta 2023.
Tsanani na ci gaba da kai wa kololuwa a shekarar da muke ta 2023. AP - Mindaugas Kulbis
Talla

Gargadin na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen da ke wannan yanki na arewacin kwallon tsakiyar Duniya su zauna cikin shirin fuskantar tsananin zafi fiye da wanda su ke gani a yanzu haka, wanda masana suka bayyana shekarar da muke ciki ta 2023 a matsayin mafi tsananin zafi da Duniya ta gani a tarihi.

Babban hukumar kula da yanayi ta Majalisar John Nairn da ke bayar da shawarwari kan yanayin tsananin zafi, ya ce yanayin zai ci gaba da tsananta kwanaki masu tsayi a nan gaba, yayinda hadarinsa ga lafiya ke ci gaba da kai wa kololuwa fiye da hasashe.

Masana a bangaren lafiya na ci gaba da gargadin al’ummomin arewacin Amurka da Turai da kuma Asiya da su kaucewa shiga rana haka zalika su guji zama cikin yanayin kishirwa ko kuma zama nesa da ruwa, bayan samun zafin da ya kai maki 48 a tsibirin Sicily da Sardinia gab da maki 48.8 mafi kololuwa da aka gani a 2021.

Nairn ya shaidawa taron manema labarai cewa yanayin tsananin zafin da akan samu bayan duk shekaru 2 zuwa 7 manuniya ce ga illar dumamar yanayi ga Duniyarmu.

Tsananin zafi kowacce shekara a irin wannan lokaci na haddasa asarar dimbun rayuka a sassa daban-daban na Duniya sai dai John Nairn ya ce yanayin zafin na yammacin tsakiyar kwallon Duniya ya rubanya zuwa ninki 6 idan na kwatanta da yadda lamarin ya ke a shekarar 1980.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.