Isa ga babban shafi

Tsananin zafi ya kashe mutane dubu 61 a Turai cikin shekarar 2022- Rahoto

Wasu alkaluman hukumar kula da lafiyar jama’a ta Tarayyar Turai ya nuna yadda mutane fiye da dubu 61 suka rasa rayukansu sakamakon tsananin zafin da nahiyar ta fuskanta a shekarar da ta gabata, inda a Faransa kadai tsananin zafin ya haddasa mutuwar kusan mutane dubu 5.

A baya-bayan nan nahiyar Turai na ganin tsananin zafin da masana ke cewa zai iya haura wanda aka gani a bara.
A baya-bayan nan nahiyar Turai na ganin tsananin zafin da masana ke cewa zai iya haura wanda aka gani a bara. AP - Matt Dunham
Talla

Alkaluman wanda hukumar ta tattara daga kasashen Turai 35 ya nuna cewa Faransa na sahun mafi wahaltuwa a sahun kasashen da tsananin zafin ya yiwa illa a bara dai dai lokacin da bayanai ke nuna yiwuwar zafin da nahiyar za ta gani a bana ya haura na barar wanda ke matsayin mafi muni a tarihi.

Rahoton da hukumar ta fitar a farkon makon nan da hadin gwiwar mujallar lafiya ta Nature Madicine wadda ta yi aikin tattara alkaluman, ta ce daga watan Mayun 2022 zuwa Satumbar shekarar an samu mace macen mutane dubu 61 da 672 cikin kasashen na Turai, wanda ya zamo mafi munin ibtila’I da nahiyar ta gani mai alaka da sauyin yanayi.

Rahoton ya ci gaba da cewa a tsakanin ranakun 18 zuwa 24 ga watan Yuli da ya zama mako mafi zafi, nahiyar ta Turai ta ga mace-macen mutanen da yawansu ya kai dubu 11 da 600 duk dai a baran.

Rahoton hukumar ya ce a Italiya kadai kasar da tsananin zafin ya fi yiwa jama’arta illa mutane dubu 18 da 10 suka mutu yayin wasu dubu 11 da 324 suka mutu a Spain kana wasu dubu 8 da 173 sai wasu dubu 4 da 807 a Faransa.

Tuni dai kwararru suka fitar da gargadin ganin cewa mutanen da ke da cutukan da basa son zafi sun kaucewa fita a cikin wannan yanayi, haka zalika dattijan da suka manyanta sai kuma kananan yara da mata masu juna biyu don kaucewa asarar rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.