Isa ga babban shafi

Tsananin zafi ya afka wa sassan Faransa da tsibirin Corsica

Matsanancin zafi ya sake afka wa yankin kudancin Faransa da kuma Tsibirin Corsica da ke daf da gabar ruwan tekun Mediterranean, yayin da masana ke cewa zafin zai ci gaba da addabar jama’a a kasashe da dama da ke kudancin Turai. 

Tsananin zafi ya tilastawa Iyalai da dama komawa rayuwa a bakin ruwa.
Tsananin zafi ya tilastawa Iyalai da dama komawa rayuwa a bakin ruwa. REUTERS - ERIC GAILLARD
Talla

Mafi yawan garuruwa da ke yankin kudancin Faransa, a yau alhamis jama’a na rayuwa ne a yanayin zafi da bai gaza maki 40 a ma’aunin Celsius ba, yayin da hatta a yankin Alpine inda ake da filayen wasa akan dusar kankara, zafi ya doshi maki 30 abin da ba saban ba. 

Ana fargabar zafin zai iya zarta maki 40 a mafi yawan birane da ke yankin kudancin Faransa, lamarin da ke tunatar da al’ummar yankin matsanancin zafin da suka yi fama da shi a shekara ta 2019, domin kuwa a wannan lokaci sai da zafin ya kai maki 45 a ma’aunin Celsius. 

Yanzu haka dai mahukunta a jihohi 8 da zafin ke yi wa barazana ciki har da Marseille, na ci gaba da yin kira ga jama’a da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin jure wa wannan zafi, yayin da ake fargabar tashin wutar daji a irin wannan yanayi. 

Mafi yawan kasashen a yankin Kudancin Turai na fama da wannan matsala, yayin da kasashen Romania, Slovakia da kuma Poland suka tura jami’an kwana-kwana domin taimaka wa Girka kashe gobarar daji da ake cewa ta samo asali ne daga wannan zafi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.