Isa ga babban shafi

Macron zai ziyarci yaran da harin wukar jiya ya rutsa da su a Faransa

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai ziyarci wadanda harin wukar jiya ya rutsa da su a yankin Annecy mai tsaunuka, harin da ya jikkata wasu ‘yan kasar ciki har da kananan yara 4 da ke dawowa daga makaranta.

Yankin da aka kai harin na jiya.
Yankin da aka kai harin na jiya. AP - Laurent Cipriani
Talla

Kowanne lokaci a yau Juma’a ne ake jiran isar shugaba Macron da maidakin Birgette zuwa yankin na Annecy, bayan da ya yi kiran hadin kai wajen tallafawa wadanda harin ya rutsa da su.

Harin na jiya wanda ya tayar da hankalin al’ummar Faransa, bayan da wani matashi mai shekaru 31 ya farwa wani wajen shakatawa dauke da wuka tare da jikkata mutane ciki har da kananan yara 4 masu shekaru 2 da zuwa 3.

An dai bayyana sunan maharin da Abdalmasih H, wanda ke matsayin dan gudun hijirar Syria da ke samun mafaka a kasar, ko da ya ke mahukuntan Paris bayan yi masa tambayoyi sun ce maharin ba da nufin ta’addanci ya kai farmakin ba, sai dai za a ci gaba da tsananta bincike akan shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.