Isa ga babban shafi

Dubban Faransawa na zanga-zangar adawa da dokar fansho

Dubban Faransawa sun sake fantsama kan tituna a wannan Talatar domin ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da matakin shugaba Emmanuel Macron na yi wa dokokin fansho kwaskwarima.

Wasu daga cikin Faransawan da suka fito gangamin adawa da dokar fansho a wannan Talatar.
Wasu daga cikin Faransawan da suka fito gangamin adawa da dokar fansho a wannan Talatar. REUTERS - STEPHANIE LECOCQ
Talla

A karo na 14 kenan tun daga watan Janairun da ya gabata da Faransawa ke gudanar da irin wannan zanga-zangar.

Bayanai na nuni da cewa, kimanin mutane dubu 600 ne suka fito gangamin na yau a fadin Faransa, adadin da ya yi karanci idan aka kwatanta da yawan mutane miliyan 1.28 da suka fito a ranar 7 ga watan Maris.

Hukumomin Faransa sun tanadi jami’an ‘yan sanda dubu 11 da suka hada da dubu 4 da aka girke a birnin Paris kadai domin sanya ido kan masu zanga-zangar ta yau.

Tun a safiyar yau aka ga dandazaon masu zanga-zanar da suka yi dafifi a shalkwatan gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta 2024 a da ke birnin Paris da zummar yin matsin lamba kan ‘yan majalisar kasar don ganin sun soke kudirin shugaba Macron na yi wa dokar fanshon gyaran fuska.

Kawo yanzu, babu wani rahoto da ke cewa, an samu tashin hankali a yayin gudanar da wannan zanga-zangar.

Shugaba Macron dai ya hakikance cewa, ba-gudu-ba-ja-da-baya, sai ya aiwatar da sabuwar dokar wadda ta kunshi tsawaita shekarun ritaya zuwa 64 daga 62.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.