Isa ga babban shafi

Wani dan kasar Syria ya kai wa yara hari a Faransa

Wani mutum dan kasar Syria da ke neman mafaka a Faransa, ya kai hari kan wata makaranta, inda ya rika cakawa mutane wuka ciki kuwa har da kananan yara.

Yadda jami'an tsaro suka mamaye kofar shiga wata makaranta da wani mutum ya kai wa hari a watan Disambar 2015 a birnin Paris na Faransa.
Yadda jami'an tsaro suka mamaye kofar shiga wata makaranta da wani mutum ya kai wa hari a watan Disambar 2015 a birnin Paris na Faransa. 路透社照片
Talla

Rahotanni daga kasar na cewa, daga cikin yaran da lamarin ya shafa har da wata karamar yarinya ‘yar Birtaniya, wadda shekarunta na haihuwa basu wuce biyu ko uku ba.

Sakataren harkokin wajen Faransa, James Cleverly wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni aka kai yarinyar asibitin Grenoble, domin bata kulawar gaggawa.

Mutumin dauke da wuka ya kai hari kan ayarin yaran da ke tsaka da wasa a filin makarantar, wanda tuni jami’an tsaro suka cafke shi.

Rahotanni na cewa, yara biyu tare da wani mutum guda suna cikin mummunan yanayi yanzu haka.

Ko da yake mutumin da aka cafke ya tabbatarwa jami’an tsaro cewa, shi mutumin Syria ne dake neman mafaka a kasar ta Faransa.

Har yanzu dai hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike kan maharin, duk da cewa ya bayyana kasar da ya fito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.